Duba abin da Gwamnonin PDP suke yi a wajen taron gangamin jam'iyar a Abuja (Hotuna)


Gwamnonin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya sun shiga ganawar sirri a wurin babban taron jam'iyyar da ke gudana yanzu haka a Abuja.

Taron na kwana biyu, ana gudanar da shi ne a dandalin Eagle Square kuma ba za a tashi ba har sai an zaɓi shugabannin jam'iyyar a muƙamai daban-daban a mataki na ƙasa.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar na cikin gwamnonin da ke yin ganawar. Kazalika tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi'u Kwankwaso na cikin ganawar.

Tuni manya da kuma masu faɗa-a-ji na PDP suka cika filin taron.

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN