Da duminsa: An sako daliban makarantar kwalejin FGC Birnin Yauri da yan bindiga suka sace a jihar Kebbi


An sako dalibai da malamai da Yan bindiga suka sace na makarantar Sakandare FGC na Birnin Yauri a jihar Kebbi. Jaridar Daily trust ta wallafa.

An sako daliban ne bayan sun shafe kwana 118 a hannun Yan bindiga. Fiye da dalibai 90 ne yan bindiga suka sace yayin wani farmaki da suka kai lokacin da daliban ke karatu a cikin makarantar.

Ranar Alhamis 17 ga watan Yuni ne yan bindiga kimanin su 150 suka farmaki makarantar Sakandare na FGC Birnin Yauri suka yi awon gaba da dalibai 90 wadanda suka hada da maza da mata da malamai uku ciki har da Mataimakin shugaban makarantar.

Daya daga cikin iyayen daliban da aka sace ne ya shaida wa Jaridar Daily trust. 

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari