Da duminsa: Kotu ta mayar da Mohammed Barau matsayin Sarkin Sudan na Kontagora


Babbar kotun tarayya dake zamanta a Minna, birnin jihar Neja ta mayar da Sarkin Sudan na Kontagora, Alhaji Mohammed Barau, kan kujerarsa bayan dakatad da shi.

A zaman da Kotun tayi ranar Laraba, ta janye umurninta na farko da tayi na haramtawa Barau gabatar da kansa matsayin Sarkin Sudan na Kontagaro na Bakwai. 

Aminiya ta ruwaito cewa lauyoyin mutum uku na farko cikin Yarimomin da suka shigar da kara kotun sun bayyanawa kotu cewa barin masarautar babu Sarki ba dace ba. Sun ce dalilin fadin haka shine Masarautar Kontagora babbar masarauta ce da ta hada kananan hukumomi shida, saboda haka bai kamata a bar ta babu sarki ba. 

Hakazalika dubi ga matsalar tsaro da ake fama a yankin. Rahoton ya kara da cewa bayan sauraron bangarorin, alkalin kotun, Mai Shari’a Abdullahi Mikailu, ya jingine umarnin da ya bayar da farko. 

Ya dage zaman shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba 2021. 

Yan takara 15 suka shigar da kara kotu Kotu a ranar Talata, 12 ga Oktoba, 2021 ta umurci Mohammed Barau Kontagora ya daina kiran kansa sabon Sarkin Sudan na Kontagora.

Wannan umurni ya biyo bayan karar ex-parte da wasu Yarimomi 15 suka shigar kotun. Wadanda aka kai kara sune Sabon Sarkin , Mohammed Barau Kontagora, Antoni Janar na jihar Neja, Kwamishanan kananan hukumomi da masarautun gargajiya.

Bayan tirka-tirka, an zabi Mohammad Barau matsayin sabon Sarkin Kontagora Bayan tirka-tirka da rikice-rikice a Masarautar Kontagora, an sanar da Muhammad Barau Kontagora a matsayin sabon Sarkin Sudan na Kontagora. 

Kwamishanan kananan hukumomi da lamuran masarautun gargajiya, Emmanuel Umar, ya bayyana hakan a jawabin da sakataren yada labaran gwamnan, Mary Berge ta saki ranar Laraba.

Source: Legit 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN