Da duminsa: An kama mutane 3 suna tsakar tone kabarin wani matashi da ya mutu , duba abin da ya faru (Hotuna)


Yansandan jihar Ogun sun kama wasu mutane uku bisa zargin tone kabari suka ciro wata gawa da dare. Wadanda aka kama su ne Sunday Aregbede, Salisu Mamud, da Bosere Rasaq.

Shafin isyaku.com ya samo cewa an kama su ne bayan sun tone gawar wani mai suna Segun Taiwo dan shekara 28 da ya mutu watanni shida da suka gabata a Unguwar Abule Sikiru da ke garin Sabo Abeokuta. 

Da misalin karfe 11:30 na dare ne wani mutum mai suna Chief Felix Obe ya gano su suna tone kabarin a cikin makabarta, sakamakon haka ya sanar wa yansanda.

Bayan samun rahotun ne, sai yansanda suka dira a makabartar kuma suka kama mutanen uku da gawar da suka tone.

Sai dai binciken farko na yansanda ya tabbatar cewa mutanen da aka kama, sun tone gawar ne domin su yi lalurar tsafi da sassan jikinta.

Kakakin yansandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce Kwamishinan yansandan jihar CP Lanre Bankole ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin a sashen bincike na CIID na rundunar. 

Gawar da suka tone daga kabari

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN