Jami'an tsaro a ranar Juma'a sun dira gidan Mary Odili, alkali a kotun koli da ke Abuja. Alkalin kotun kolin mata ce ga Peter Odili, tsohon gwamnan jihar Ribas wanda a halin yanzu ya ke cikin wadanda hukumar yaki da rashawa ta kasa, EFCC suka sanya wa ido.
Kamar yadda TheCable ta wallafa, Har yanzu dai babu cikakken bayani kan abinda ke faruwa a gidan.
Kamar yadda wata majiya ta ce, jami'an tsaron da suka tsinkayi gidan sun hada da jami'an 'yan sanda da na sojojin Najeriya.
Har a yayin rubuta wannan rahoton, ba a san dalilin da yasa jami'an tsaron suka shiga gidan alkalin ba,
TheCable ta wallafa. Alkalin wacce a halin yanzu ita ce mafi daraja ta biyu a alkalan kotun kolin, ana tsammanin za ta kasance cikin alkalai bakwai da za su sanar da matsayar karshe kan rikicin harajin da ya shafi jihohi da gwamnatin tarayya.
Karin bayani na nan tafe...
Source: Legit
Rubuta ra ayin ka