Da Dumi-Dumi: 'Yan bindiga sun harbe sarakuna biyu har lahira a wurin taro


Masarautun gargajiya a jihar Imo sun shiga zaman makoki sakamakon kashe wasu sarakuna biyu da aka yi. Daily Trust ta ruwaito cewa sarakunan biyu sun tafi hallartar taron masu ruwa da tsaki ne a Nnenasa, hedkwatar karamar hukumar Njaba na jihar a lokacin da bata garin suka kai hari.

Sarakunan da abin ya shafa sune Eze E. A Durueburuo, Obi I na Okwudor, da Eze Sampson Osunwa na garin Ihebinowere.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng! Rahoton na Daily Trust ya kuma bayyana cewa wasu masu rike da sarautun gargajiyar sun bar wurin da raunuka daban-daban.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Imo, Mike Abattam ya tabbatar da rasuwar sarakunan biyu. Ya ce an tabbatar da mutuwarsu nan take a wurin yayin da wadanda suka jikkata kuma an garzaya da su asibiti domin basu kulawan likitoci.

Gwamnan Imo Hope Uzodinma ya yi Allah-wadai ta harin Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, yayin hira da ya yi da Channels Television ya yi tir da kisar ya kuma jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa.

Ya yi alkawarin za a gudanar da bincike don gano wadanda ke da hannu a kuma hukunta su daidai da laifinsu. Har wa yau, gwamnan ya yi kira ga al'ummar jiharsa su kwantar da hankulansu domin gwamnati tana bin didigin lamarin.

Harin shine na baya-baya cikin muggan hare-hare da ake kai wa a jihohin kudu maso gabas. A ranar Lahadi, yan bindiga sun kai hari hedkwatar yan sanda a jihar Ebonyi sun kashe jami'i daya sun kona motoccin sintiri. Ana alakanta hare-haren na baya-bayan da kungiyoyin masu neman ballewa daga Nigeria.

Source: Legit.ng

Masarautun gargajiya a jihar Imo sun shiga zaman makoki sakamakon kashe wasu sarakuna biyu da aka yi. Daily Trust ta ruwaito cewa sarakunan biyu sun tafi hallartar taron masu ruwa da tsaki ne a Nnenasa, hedkwatar karamar hukumar Njaba na jihar a lokacin da bata garin suka kai hari. Read more: https://hausa.legit.ng/news/1439453-da-dumi-dumi-yan-bindiga-sun-bindige-sarakuna-biyu-har-lahira-a-wurin-taro/

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN