Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun fasa gidan yari a jihar Oyo, Sun saki fursunoni duk


Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wasu tsagerun yan bindiga sun kai hari gidan yarin dake Abolongo, a jihar Oyo ranar Jumu'a da daddare. 

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin gidan yarin, sannan duka saki dukkan fursunonin dake ciki. 

Miyagun yan bindigan sun fasa gidan yari ne da tsakar dare, inda suka yi amfani da gurneti wajen tilasta samun damar shiga harabar gidan gyaran halin. 

Harin ya jefa gidan gyaran halin cikin mawuyacin hali, yayin da masu gadin wurin suƙa watse domin neman hanyar tseratar da rayuwarsu.

Source: Legit.ng 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN