Barayin waya a kan adaidaita sahu sun hallaka matashi a Kano, duba yadda lamarin ya faru


Wasu masu kwacen waya a kan babur din Adaidaita Sahu sun hallaka wani matashi a Kano dan asalin Karamar Hukumar Fagge.

Matashin, mai suna Abdullahi Bala, mai kimanin shekara 30 ya gamu da ajalinsa ne ranar Juma’a bayan ya taso daga aiki a tsakanin titin Zungeru Road zuwa Festing Road.

Wani dan uwan mamacin wanda ya ce tare suka taso, Yazid Ali Fagge wanda ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin ya ce an kashe marigayin ne da misalin karfe 6:45 na yammacin Juma’a.

Ya ce, “Ya hau babur din Adaidaita Sahu da niyyar zuwa ta’aziyya a unguwar Birget, ashe bai san wadanda ya hau babur din nasu barayi ba ne.

“Sai suka ce ya basu wayar shi, amma sai ya jefo ta waje da nufin mutane su gani ko za su kawo masa dauki. Ana cikin haka sai suka buga masa wani karfe a cinyarsa, sannan suka gudu.

“Hakan ne ya sa mutanen wajen suka ankarar da ’yan sanda, inda su kuma suka fara tare duk mai Adaidaita Sahun da aka gani da goyon gefen direba.

“A haka aka tare mutane da dama, amma babu wanda zai iya gane su wanene suka aikata laifin.

“Daga nan ne ’yan sanda suka kai shi Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, amma mu ’yan uwansa sai ranar Asabar ma sannan muka sani ta hanyar ’yan sandan. Mu dai kawai mun san ya bata. Yanzu ma ban jima da dawowa daga jana’izarsa ba,” inji Yazid.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce tuni suka cafke mutum biyu bisa zargin aikata laifin kuma suna shirin gurfanar da su a gaban kotu.

A cewarsa, suna ci gaba da fadada bincike don gano sauran masu hannu a aikata ta’asar

Leadership Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN