Type Here to Get Search Results !

Bakar aniya: An damke budurwa da ta saki bidiyon lalata da tsiraici na babban ma'aikacin Gwamnati domin ya ki ya bata N15m da ta nema (Hotuna)


An gurfanar da yarinya yar shekara 19 da ta yi kokarin bata sunan tsohon Sakataren din-din-din na ma'aikatar ilimi na jihar Bayelsa Dr. Walton Liverpool ta hanyar sakin bidiyonsa tsirara. Shafin isyaku.com ya wallafa

Yarinyar mai suna Miss Charlotte Delhi, yar shekara 19 ta nemi Dr. Walton ya biya ta N15m ko ta saki bidiyon lalata da ya yi da ita. Sai dai ya ki ya bata kudin, sakamakon haka yarinyar ta saki faifen bidiyon a shafukan sada zumunta.

Bayan jami'an rundunar DSS na jihar sun gudanar da bincike kan SIM card da ta yi amfani da shi wajen aika sakon a shafukan sada zumunta, daga bisani bincikensu ya kai su ga Chartllotte Delhi kuma suka damke ta. Ta ce shekarunta 15 lokacin bincike, amma takardar haihuwarta su nuna cewa shekarunta 19 ne.

Hotuna sun bayyana yadda jami'an gidan gyara hali suka iso da ita Kotu.

Kalli hotuna:
Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies