Babbar Magana: Gwamnatin Shugaba Buhari ta yi barazanar kafa dokar ta baci a wata jihar, duba ka gani


A ranar Laraban nan, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata iya kafa dokar ta baci a jihar Anambra idan akwai bukatar hakan, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

A cewar gwamnatin shugaba Buhari, zata ɗauki duk matakin da ya dace domin tabbatar da an gudanar da zaɓen 6 ga watan Nuwamba a jihar.

Antoni Janar, Abubakar Malami, shine ya faɗi haka yayin da yake amsa tambayoyin manema labari jima kaɗan bayan taron FEC a fadar shugaban ƙasa.

Bugu da ƙari, Malami yace ba abinda gwamnati ba zata yi ba wajen tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.

Me FG ta shirya yi domin zaɓen Anambra?

Ministan shari'a, Malami, yace:

"Matukar aka farmaki tsaron mu na ƙasa, kuma muka samu barazana a demokaraɗiyya, to zamu yi duk abiɓda ya dace."

"A matsayin mu na gwamnati, haƙƙin mu ne tabbatar da bin doka da oda kuma hakkin mu ne tsare rayuwar al'umma da dukiyoyinsu."

"Saboda haka, busa waɗannan nauye-nauye da kundin tsarin mulƙi ya ɗora mana, ba hanyar da ta dace da bazamu bi ba."

Zamu yi duk abinda ya dace - Malami

Ministan ya kara da cewa gwamnati ta shirya yin duk abinda ake bukata domin tabbatar an gudanar da zaɓen gwamnan jihar Anambra.

"Ba abinda ba zamu iya ba, har da kafa dokar ta baci. Saboda haka matsayar mu a gwamnatance shine zamu samar da jami'an tsaro domin tabbatar da an yi zaɓen."

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN