Ba wani mahaluki da ke bukatar soyayya da hidima kamar cin gashin-kan ka Aliyu H.

Daga Aliyu H. Sokoto

Abu ne mai kyau ka mutunta, ka kyautata, ka girmama ka kuma yi biyayya ga duk wani babba da Allah ya hada ka da shi, malami ne ko dan siyasa ko kuma ubangida a sana'a. Amma abu mafi muhimmanci mu sani shi ne, duk duniya babu wani mahaluki dake bukatar soyayya da hidima kamar qashin-kan ka.

Hausawa suka ce amfanin rai yafi ga mai shi, duk gatar da wani zai maka idan kai bakaiwa kan ka gata ba aikin banza ne gatan don ba zata amfanar ba, duk mutuncin wani da ka kare idan kai ka rasa naka mutumcin a kan kare mishi to ka fadi a wannan kasuwar. Babu hankali, basira ko tunani ga duk wani matashin da ya lamunce ya rusa katangar shi ya debi kasar yaje ya gina katangar wani don kawai tunanin za a baka wani abu da bai zai gina maka taka katangar ba.

Sannu-Sannu zaku taka matakin da suka taka, na shekaru ko na muqami ko na ilimi idan a duniyar karatu ne, yaya kuke gani idan kimar ku da martabar ku ta riga ta sulale a lokacin da kake gina ta wasu. Ya kuke gani idan aka tashi ranan alkiyama Allah ya kama ku da laifin karya, yarfe, cin mutuncin masu mutunci da na juna kawai don wani mahaluki? Lalle ya kamata mu canza tunani, kafin kare wani mu kare kan mu, kafin taimakon wani mu taimaki kan mu, sannan kuma mafi muhimmanci kafin wani ya mana gata muyiwa kan mu gata.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN