Ba wanda zai tilasta wa ƴan arewa zaɓen ɗan kudu


Ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya ta ce babu wanda zai tilasta wa al`ummar yankinta zaɓen wani dan takarar shugaban kasa da ya fito daga kudancin ƙasar a zaben 2023.

Ƙungiyar ta mayar da martani ne ga matakin da ƙungiyar gwamnonin kudancin Najeriya da wasu ƙungiyoyi suka ɗauka cewa lokaci ya yi da mulki zai koma bangarensu.

Kakakin kungiyar dattawan na arewa Dr Hakeem Baba Ahmed ya shaida wa BBC cewa arewa tana da yawan masu zabe, don haka "yankin ba ya shakkar ko wace irin barazana."

A wani taron da gwamnonin kudancin Najeriya suka gudanar a watan Yuli sun ce dole shugabancin Najeriya ya kasance na karɓa-karɓa daga yankin arewaci zuwa kudanci, kuma suna son shugaban ƙasa da za a zaɓa a 2023 ya fito daga yankin kudancin ƙasar saboda abin da gwamnonin suka kira tabbatar da adalci.

Kasancewar Najeriya mai bambancin kaɓilu da addinai, bisa al'ada jam'iyyun siyasa kan yanke shawarar yin karɓa-karɓa tsakanin yankin arewaci da kudanci. Kuma mutanen yankin kudanci na ganin yanzu lokacinsu ne, kasancewar yanzu shugaban da ke mulki ya fito ne daga yankin arewaci.

Sai dai kuma ƙungiyar dattawan arewa mai tunƙaho da yawan jama'a a Najeriya ta ce ana nuna wa yankin yatsa da maganganu masu zafi cewar ko da tsiya ko da arziki sai mulki ya koma kudu.

"Idan ƴan kudu na kwaɗayin a jefa masu kuri'a, ba zagi za su yi ba, ko suce a yi ko a mutu - ba kuma irin wannan izgili zai sa mu ji tsoro mu ce a zabi ɗan kudu ba.

"Ba mu ce ba mu son ɗan kudu shugaban kasa ba, amma irin barazana da bada tsoro shi ne ba za mu yarda da shi ba," in ji Dr Hakeem Baba Ahmed.

Ya ƙara da cewa mulkin dimokuradiya ake yi, ko da yan siyasa sun je sun yi yarjejeniya, mutane ne za su jefa kuri'a, kuma mutanen arewa suna da zaɓi ko su zaɓi ɗan kudu ko ɗan arewa.

"Huruminmu ne kan wanda za mu zaɓa, ba na jam'iyyu ba, aikinsu kawai su tsayar da ƴan takara - amma su sani akwai alkiblar da mutanen arewa suka sa a gaba,"

Ya kuma ce yankin arewa ba ruwansa da ra'ayin manyan jam'iyyun siyasa APC da PDP. "Abin da yake da amfani shi ne muna tuna masu duk abin da za su yi ko su kitsa - idan arewa ta ga dama ɗan arewa za ta zaɓa, ba wani wanda zai tafi ya shirya ya zo ya ce wa yan arewa su zabi dan kudu."

"Ba za mu goyi bayan wata jam'iyya da za ta sayar da 'yancinmu ba ko kuma a yi wata yarjejeniya," in ji kakakin ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya Dr Hakeem Baba Ahmed.

Ya kuma ce zaɓen 2023 kamar jihadi ne ga ƴan arewa domin ƙwatar kansu da ga matsaloli na rashin tsaro da talauci da rashin ayyukan yi. "Za mu yi amfani da yancinmu - muna ganin matsalolin da muke da su dole sai ɗan arewa zai yi maganinsu."

"Sai mun ga dama za mu zaɓi dan kudu amma ba da tsiya da zagi ba. muna iya yarda mu zabi dan kudu amma sai yan arewa sun tabbatar da zai yi shugabancin da ya fi waɗanda muke da su a yanzu," in ji shi.

BBC Hausa

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN