Asiri ya tonu wajen rabon kudin fansa tsakanin mai gadi da ya yi hayan masu sace mutane suka sace uban gidansa da wasu mutum 3


Rundunar yansandan jihar Edo ta kama wani mai gadi mai suna Best Abarawe sakamakon hada baki da masu satar mutane suka sace Manajan kampani da yake wa gadi a birnin Benin. Shafin isyaku.com ya ruwaito.

Yan sanda sun kama Abarawe tare da masu sace mutane da suka hada da Jacob Goto da Akpadulaha Yamoh. 

Abarawe ya hada baki da masu sace mutane suka sace Manajan kampani da yake aiki tare da wasu mutum uku da suke sana'ar Manajan ma'aikatan hakan yashi kuma suka karbi kudin fansa.

Sai dai asiri ya tonu tsakaninsa da masu sace mutane sakamakon jayayya wajen rabon kudin da suka karba na fansar wadanda suka sace.

Bisa wannan dalili yansanda suka kama shi tare da masu sace mutanen.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN