Ash sha: Tsoho mai shekara 71 ya yi mutuwar gaggawa yayin da yake tsakar yin zina da karuwa a dakin Otel


Wani tsoho dan shekaraa 71 mai suna Ajibola Olufemi Adeniyi, ya mutu yayin da yake tsakar yin zina da wata karuwa a cikin dakin wani Otel a jihar Ogun. Shafin isyaku.com ya wallafa.

Lamarin ya faru ne ranar Litinin a wani Otel da ake kira 50/50 hotel da ke garin Ogijo a karamar hukumar Sagamu na ihar Ogun.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa tsohon da ke zaune a gida mai lamba 22, Akilo Street, da ke unguwar Bariga ya ziyarci Otel din ne tare da wata karuwa mai suna Joy domin ya shakata.

Wani da ke zune a kusa da wajen da Otel yake, da baya son a ambaci sunansa, ya ce yayin da tsohon ke tsakar yin zina da karuwar, sai ya yanke jiki ya fadi ya mutu nan take.

Yansanda daga ofishin yansanda na Ogijo sun ziyarci wajen da lamarin ya faru kuma suka dauke gawar. kuma suka tafi da katin ATM da Lasisin tukin mota da suka samu a jikin tsohon.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN