An yi wa Pasto dukan fitan albarka bayan an yi zargin ya saci wayar salula (Hotuna)


Wasu matasa sun wulakanta wani Pasto bayan sun yi zargin cewa ya saci wayar salula. Shafin isyaku.com ya wallafa.

Sun yi zargin cewa Paston ya saci wayar ne a Unguwar NNPC Mega station kan hanyar Otukpo a birnin Makurdi na jihar Benue ranar 18 ga watan Oktoba. Sai dai shaidu sun kasa tabbatar da satar.

Tuni dai matasan suka yi wa Pasto rauni har jini yana fitowa a fuskarsa. 


Previous Post Next Post