An yanke wa Salisu ɗaurin gidan yari kan satar tukwane da kujeru a coci


An yanke wa wani hukuncin dauri a gidan yari kan satan tukwane da wasu kaya a coci. Hoto: Daily Trust

Ya ce Salisu ya kutsa cikin cocin ya sace manyan tukwane biyu na aluminium, tukwanen soye-soye, kujerun roba biyar, kwanuka biyu da wasu karafa na mimbari da kudinsu ya kai N300,000.

Kamar yadda ruwaiyar ta NewsWireNGR ta bayyana, Alkalin kotun, Mrs M.I. Dan-Oni ya yanke wa wanda aka gurfanar hukunci bayan ya amsa aikata laifukan da ake tuhumarsa.

Dan-Oni wacce bata bashi zabin biyan tara ba, ta kuma kara masa da ayyuka masu wahala.

Wanda ake yanke wa hukuncin yana zaune ne a gida mai lamba 9, Seriki St., Idi-Araba, Mushin, Lagos kuma an gurfanar da shi a kotun ne a ranar 9 ga watan Yuli kan zargin sata.

Laifin sata ya saba wa sashi na 287 na dokar masu laifi na jihar Legas ta shekarar 2015.

Jerin sunayen 'yan Nigeria 11 da aka kama a Amurka kan almundahar kudi da damfarar mutane fiye da 50

A baya, kun ji cewa Hukumar binciken shari'a na Amurka ya gurfanar da wasu 'yan Nigeria 11 a kotu kan zarginsu da hada baki wurin aikata almundahar kudade, damfara ta banki da satar kudade da sunan wasu.

A ranar Laraba ne Attoni na Kudancin New York, Damian Williams da Jam'in FBI mai kula da New York, Patrick J, Freancy suka sanar da sunayen 'yan Nigeria 11 da ke da hannu wurin karkatar da miliyoyin daloli daga damfarar imel da damfarar soyayya.

Hukumar binciken shari'a na Amurka ta bayyana hakan a ranar Laraba kamar yadda ya zo a ruwayar SaharaReporters.

Source: Legit.ng

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN