An yanka ta tashi: 'Ni ne shugaban kungiyar Mawakan APC na jihar Kebbi' Inji Bello Aljannare


Alh Bello Bala Aljannare ya ce korar da wasu manbobin kungiyar Mawakan jam'iyyar APC na jihar Kebbi suka ce sun yi masa zazancen wofi ne kawai. 

A zantawa da wakilin shafin labarai na isyaku.com ya yi tare da shi a garin Birnin kebbi ranar Talata 19 ga watan Oktoba, Bello Aljannare ya ce "Abin da ya faru matsala ce ta cikin gida. Kuma wadanda suka ayyana waccan matakin sun yi ne a kan kuskure sakamakon wata yar gibi da aka samu wajen isar da sako tsakanin yan kungiya. Amma abin da suke zargi ba gaskiya bane".

Bello ya kara da cewa " Ni ne shugaban kungiyar Kebbi state APC Musician Forum, kuma takardar rijistan kungiya na wajena. Ni ne na kirkiro kungiyar, kuma na assasata, daga bisani na jawo sauran mawaka suka shigo kungiyar ".

Sai dai wani bincike da shafin labarai na isyaku.com ya gudanar dangane da lamarin, ya nuna cewa yanzu haka masu ruwa da tsaki tare da jiga-jigan jam'iyyar APC na jihar Kebbi basu aminta da yunkuri da wasu manbobin kungiyar mawakan suka yi ba yayin da aka dukufa wajen dinke kowace irin baraka tsakanin yan kungiyar. 

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN