Ɗan sanda da ya kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugabannin APC a Kano ya ta da kura


Rundunar 'yan sanda Najeriya ta umarci a binciki wani jami'in ɗan sanda da hotunansa ke yawo a kafofin sada zumunta yana kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugabannin jami'iyyar APC na Kano.

Hotunan da suka karaɗe shafukan sada zumunta na nuna jami'in tsaye kusa da Abdullahi Abbas sabon zaɓaɓɓen shugaban APC tsagin Ganduje.

A wata sanarwa da ta fitar, kakakin 'yan sanda Zone One a Kano, Abubakar Zayyanu, ya ce mataimakin babban sufeta 'yan sanda da ke kula da shiyya ta ɗaya, AIG Abubakar Sadiq Bello ne ya umarci a binciki ɗan sandan.

A cewar AIG abin da aka hango ɗan sandan na aikatawa ya saɓa ka'idojin aiki.

Wannan batu dai ya yi ta ja hankali da haifar da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda mutane suka rinƙa diga aya kan aikin jami'an tsaro da alaƙarsu da siyasa.

Me sanarwar ta ƙunsa?

Rahotanni na cewa ɗan sandan wanda aka bayyana shi da Bashir Mohammed na aiki ne a fadar gwamnatin Kano, inda kuma daga can aka tura shi domin aiki tare da shugaban APC na Kano.

Sanarwar yansanda

Sanarwar ta kuma shaida cewa, "An ja hankalin mataimakin babban sufeta na kasa shiyya ta ɗaya a Kano kan wani hoto da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke nuna jami'in ɗan sanda na kaɗa kuri'a a zaɓen shugabannin APC da aka gudanar a Kano da wasu manyan 'yan siyasa, da shugaban jam'iyya, Abdullahi Abbas".

"An bayyana ɗan sandan a matsayin Bashir Mohammed wanda ke aiki da sashin ba da kulawa ta musamman, shiyya ta ɗaya a Kano.

"Ɗan sandan na aiki a fadar gwamnatin Kano, inda kuma aka tura shi domin aiki tare da Abdullahi Abas.

"Bisa ga ɗabi'un da ya nuna na rashin ɗa'a, AIG ya umarci a tura rahotansa sashen bincike na shiyyar.

"Idan aka samu ɗan sanda na aikata abin da ya saɓa dokokin aiki, za a ɗau matakan ladabtarwa a kansa."

Mataimakin sufetan ya sanar da al'umma cewa za su yi duk abin da ya dace kuma za a sanar da al'umma mataki ko hukuncin da aka yanke biyo bayan bincikensu.

Me mutane ke cewa?

Mutane a shafukan sada zumunta musamman Facebook sun yi ta yaɗa hoton suna bayyana mabambantan ra'ayoyi kan yada jami'in tsaro ke jefa kansu cikin siyasa.

Akwai wasu kuma da ke ɗiga ayar tambaya da mamaki ganin yadda wannan jami'in ke kaɗa kuri'a ko a jikinsa.

Keta haddin dimokuradiya a matakin kololuwa. Sanye da kayan 'yan sanada an iske yana kada kuri'a a zaben shugabanni APC tsagin gwamnatin Kano.

Ƙarin haske

Jihar Kano na daga cikin jihohin da zaben shugabannin jam'iyyar APC mai mulkin kasar, wanda aka gudanar a matakin jihohi ya bar baya da kura, sakamakon yadda bangarori daban-daban ke ikirarin cewa su ne halatattun wadanda ya kamata su gudanar da wadannan zabuka.

An gudanar da zaben a wurare biyu daban daban inda aka ja layi tsakanin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da kuma tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahin Shekarau.

A ranar Asabar da ta gabata ne dai uwar jam'iyyar APC ta amince a gudanar da zaben shugabannin jam'iyyar a matakin jiha.

Kuma Barista Auwalu Abdullahi shugaban kwamitin gudanar da zaben shuwagabannin jam'iyyar APC a matakin jihar da uwar jam'iyyar APC a Najeriya ta aika Kano, ya bayyana cewa Abdullahi Abbas ne ya yi nasara da kuri'u 3,122 hakan ya bashi damar zama sabon shugaban jam'iyyar APC na jihar.

To sai dai tsagin da ke rikici da bangaren gwamnan Kano karkashin jagorancin sanata Ibrahim Shekarau su ma sun gudanar da nasu zaben a Janguza a yankin karamar hukumar Tofa dake jihar, inda suka zabi Alhaji Ahmad Haruna Zago a matsayin na su shugaban jam'iyyar.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN