An fitar da jerin Musulmi 500 mafi ƙarfin faɗa aji a duniya, Buhari, Ɗangote, Ɗahiru Bauchi da Zakzaky na ciki


Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari yana cikin jerin musulmin duniya 500 mafi karfin fada aji kamar yadda cibiyar nazarin addinin Islama da ke Amman a Jordan ta fitar.

A kowane shekara cibiyar tana fitar da sabbin sunayen musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya.

Shugaba Buhari ne mutum na 16 a cikin jerin sunayen musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya a bana kamar yadda The Muslim 500 ta fitar.

Jerin sunayen musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya, Buhari da Dahiru Bauchi da Dangote na ciki

Musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya, Buhari da Dahiru Bauchi da Dangote na ciki. Hoto: The Muslim 500 Source: Facebook

Sauran 'yan Najeriya da ke cikin jerin sunayen sun hada da Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III, Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Sheikh Ibrahim Saleh.

Alhaji Aliko Dangote, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Sheikh Yakubu Musa Katsina, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky suma suna ciki.

Jerin sunayen musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya, Buhari da Dahiru Bauchi da Dangote na ciki

Shugaba Muhammadu Buhari ne na 16 cikin jerin musulmi 500 masu fada aji. Hoto: The Muslim 500 Source: Facebook

Jerin sunayen musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya, Buhari da Dahiru Bauchi da Dangote na ciki

Musulmi 500 mafi karfin fada aji a duniya, Buhari da Dahiru Bauchi da Dangote na ciki. The Muslim 500 Source: Facebook

A cewar cibiyar:

"Duk wani da ke da karfin fada aji ko ta gargajiya, akida, kudi, siyasa ko waninsa kuma zai iya kawo canji a duniyan musulmi yana iya fadowa cikin jerin.

"Fitar da sunayensu baya nufin muna goyon bayan ra'ayoyinsu ko akidunsu, kawai dai abin da ake duba wa shine karfin fada aji da suke da shi."

Mutane mafi karfin fada aji a duniyar musulmi

A cewar Muslim 500, Dan kwallon Liverpool, Mohammed Salah, Sadio Mane, Paul Pogba, Zinedine Zidane suma suna cikin jerin masu karfin fada aji.

Amma wadanda ke kan gaba a jerin sun hada da

Shugaba Recep Tayyip Erdoğan, Shugaban kasar Turkiyya

Sarki Salman bin Abdul-Aziz Al-Saud na kasar Saudiyya

Ayatollah Hajj Sayyid Ali Khamenei, shugaban jamhuriyar musulunci ta Iran

Sarki Abdullah II Ibn Al-Hussein na kasar Jordan

Mai shari'a Sheikh Muhammad Taqi Usmani, malami kuma shugaban Deobandi

Sarki Mohammed VI, Sarkin kasar Morocco

Mai martaba, Janar Sheikh Mohammed bin Zayed Al-Nahyan, yarima mai jiran gado na Abu Dhabi kuma mataimakin babban kwamandan sojojin UAE

Ayatollah Sayyid Ali Hussein Sistani, Marja na Hawza, Najaf da Iraq

Sheikh Al-Habib Umar bin Hafiz, Shugaban Dar Al Mustafa, Tarim, Yemen

Sheikh Salman Al-Ouda, Mai wa'azi kuma makaranci

Legit Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN