An dasa wa dan Adam kodar alade kuma ya yi aiki a kasar Amurka, duba yadda ta faru


A karon farko a kasar Amurka, Likitoci sun yi nassarar dashen kodar alade da aka yi wa kwayoyin halittarsa kwaskwarima a jikin dan Adam kuma ya yi aiki dai dai.

Likiticin sun tafiyar da wannan aiki ne a NYU Langone Health a birnin New York.

Wanda aka yi wa dashen kodar mace ce da ta kamu da mutuwar kwakwalwa sakamakon cutar Koda. Yan uwanta sun aminta da ayi wannan gwaji a jikinta.

Likitoci sun dasa mata kodar, kuma suka fitar da shi a waje domin su nazarci yadda yake aiki har tsawon kwanaki uku. 

Sakamakon da suka samu na fitsarin da ya fito daga kodar ya numa cewa ba matsala, alhalin kodarta na asali na dauke da sinadarin Creatinine, wanda ke nuna cutar Koda a cewar Dr Robert Montgomery, jagoran Likitocin dashe da suka gudanar da aikin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN