Ababen da ya kamata ku sani dangane da kungiyar "Arewa Media Writers" reshen jihar Kebbi


Ƙungiyar Marubutan Arewa A Kafofin Sadarwar Zamani "Arewa Media Writers" Reshen Jihar Kebbi, Ta Gudanar Da Gagarumin Taron Tattaunawa Na Masu Ruwa Da Tsaki Na Ƙungiyar

Daga Ƙungiyar "Arewa Media Writers" 

Ƙungiyar Marubutan Arewa a Kafofin Sadarwar Zamani "Arewa Media Writers" reshen Jihar Kebbi, ta gudanar da gagarumin taron tattaunawa da sada Zumunci da kuma wayar da kan 'Yayan kungiya a karo na biyu wanda ya gudana a jiya Lahadi, 03-10-2021.

An gudanar da taron ne a ɗakin taro dake makarantar "Basaura Institute of Comprehensive Education" (B.I.C.E) dake garin Birnin Kebbi, a ƙarƙashin jagorancin shugaban Ƙungiyar reshen Jihar Comrd Abubakar Umar Gwadangaji.

A yayin gudanar da taron, an tattauna muhimman abubuwa da dama da suka shafi Ƙungiyar tare da fitarda hanyoyin da za'abi wajen kawo ƙarshen yaɗa labaran da basu inganta ba, da kuma fitowa da hanyoyin da za'a bi domin kawo wa Ƙungiyar cigaba da haɗin kan marubutan Arewa da kuma al'ummar Arewa baki ɗaya.

Shugaban ƙungiyanm4 Arewa Media Writer's Kebbi State Comrd Abubakar Umar Gwadangaji, yayi jawabai masu muhimmanci wajan haɗin kai da kuma yiwa sabbin Membobi marhaban da shigowa wanna ƙungiyar da kuma karanta masu kundin tsarin tafiyar da ƙungiyar.

Haka kuma manyan masana 'Yan jaridu da kuma marubuta na musamman waɗanda suka samu damar halartar taron sun haɗa da;

1. Muhammad Basharu, Chairman "Arewa Media Writers" reshen Jihar Sokoto.

2. Alh Abubakar Dallatun Kalgo (Dan Jarida kuma Masani a harkar rubuce-rubuce).

3. Shehu Usman Shyman, Chairman Voice of Kebbi State.

4. Isiyaku Garba Zuru (Isiyaku Sinora, isiyaku.com) Dan Jarida kuma Masani a harkar media.

A yayin taron tattaunawar da Ƙungiya ta shirya, an samu damar gayyato 'Yan jaridu da kuma masana akan harkar Rubuce-Rubuce da kuma Social Media, waɗanda suka baɗa haske da jan kunne da kuma shawarwari akan sha'anin rubutu a Social Media da kuma sauran kafafen yaɗa labarai.

An gabatar da Addu'o'i na musamman domin nemawa ƙasarmu Najeriya da Jahar mu ta Kebbi zaman lafiya.

Da karshe, Ƙungiyar "Arewa Media Writers" tana buƙatar Addu'o'in ku, A kan muhimman ayyukan da ta saka a gaba na ganin ta tsaftace harkar Rubuce-Rubuce a kafofin sadarwar zamani.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN