Yanzu-Yanzu: 'Yan sanda sun cafke wadanda suka kashe mahaifin gwamnan Filato


Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wadanda suka kashe Pa Defwan Dariye, mahaifin tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye, inji rahoton jaridar Punch.

Jaridar legit Hausa ta rewaito cewa an kashe dattijon dan shekara 93 bayan da masu garkuwa da mutanen suka sace shi suka kuma karbi kudin fansa miliyan 10 daga iyalansa.

Jagoran gungun masu garkuwa da mutane, Jethro Nguyen, dan shekara 53, ya ce ya dauki hayar wasu mutane 10 ciki har da wasu Fulani makiyaya don sace tsohon a gidansa, ya kara da cewa sun tsare shi a maboyarsu na kusan kwanaki 10 kafin su hallaka shi.

Nguyen, wanda aka gabatar da shi a hedkwatar rundunar sanda a Abuja, ranar Laraba 8 ga watan Satumba, ya furta cewa ya ba daya daga cikin 'yan tawagarsa umarnin harbe tsohon.

Ya ce sun yi garkuwa da mamacin ne saboda za su iya samun kudi cikin sauki daga gareshi kasancewar dansa ya taba yin gwamna a jihar Filato, kuma sanata a Najeriya.

Karin bayani na nan tafe..

Source: Legit.ng

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari