Yanzu yanzu: Miji ya kama kato turmi tabarya kan matarsa bayan ya buge kofar dakin Otel, duba abin da ya faru


Asirin wata mata ya tonu bayan mijinta ya kamata turmi tabarya tare da wani kwarto a dakin Otel.

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa mijin matar ya dade yana zargin matarsa da bin maza a waje. Sai dai saboda rashin hujja ya yi hakuri.

Sakamakon haka mijinta ya sa ido kan harkokinta na zirga-zirga. Sai dai daga bisani dubu ta cika, domin mijinta ya sami labarin cewa matarshi tana cikin dakin Otal tare da wani kato. Lamarin ya faru ne a jihar Delta.

Nan take mijin ya isa dakin Otel ya buge kofa kuma kiri kiri ya kama wani mutum turmi tabarya a kan matarsa.

Lamari da ya sa mijinta ya yi wa katon mugun duka, tare da kunyata shi. Daga bisani kwarton ya duka ya yi ta ba mijin matar hakuri ya ce bai san cewa matar aure ba ce, domin bata gaya mashi cewa tana da aure ba.

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE