Type Here to Get Search Results !

Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa ta nemi Buhari ya fitar da N300bn don gyaran tituna a Neja


Majalisar dattijai a ranar Talata ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da Naira biliyan 300 a matsayin kudin taimakon gaggawa don gyara munanan hanyoyi a jihar Neja.

Wannan kuduri na babban zauren ya biyo bayan wani kudiri kan lalacewar hanyoyi a fadin jihar Neja da toshe hanyoyin ta hanyar nuna rashin amincewa da direbobin tirela da direbobin tanka suke yi a cikin kwanaki hudu da suka gabata.

Mataimakin Babban Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Aliyu Sabi Abudullahi, mai wakiltar Neja ta Arewa ne ya kawo kudirin, in ji rahoton The Nation.

A cikin gudunmawarsa, Sanata Mohammed Sani Musa, ya zargi Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola, da nuna son kai a aikinsa na gina hanyoyi da gyaran hanyoyi a jihar Neja.

Karin bayani na nan tafe...

Source: Legit.ng

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Hollywood Movies