An gurfanar da korarren dansandan nan Sgt. Samuel Phillips a gaban Kotun Majistare bayan ya kashe wata yarinya yar shekara 18 ranar 11 ga watan Satumba, mai neman gurbin shiga Jami'a mai suna Monsura Ojuade a Unguwar Ijeshatedo a Surulere da ke Birnin Lagos.
An gurfanar da shi ne sanye da jar taguwa mai gajeren hannu da wando Jeans mai kalar bula mai duhu, sanye da hular Cape, a gaban Alkalin Kotun Majistare da tsakar ranar Juma'a .
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI