Yanzu-yanzu: Bayan kwanaki 6 hannunsu, yan bindiga sun saki yayan sakataren jihar Katsina


Kabir Muhammad, Yayan sakataren gwamnatin jihar Katsina, Muhammad Inuwa, da aka sace ranar Larabar da ta gabata, ya samu yanci bayan kwanaki shida.

Mai magana da yawun Inuwa, Kabir Yar'adua, ya tabbatar da hakan ranar Talata, rahoton Punch.

Yace:

"Lallai an saki dattijon amma babu kudin da aka biya na fansa."

An samu labarin cewa an saki dattijon ne bayan damke wasu masu kaiwa yan bindiga bayanai a jihar, cikinsu har da mahaifin shugaban yan bindigan.

Majiyoyi sun bayyana cewa an tuntubi yan bindigan cewa an damke mahaifin shugabansu, sai yan bindigan suka yarsa a sake yayan SSG Inuwa.

Wata majiya ta bayyana cewa,

"Yan bindigan sun saki Yaya Muhammad da daren Litinin kuma ya koma wajen iyalansa."

"Ba'a kudin fansa ba, saboda mun saki mahaifin shugaban yan bindigan a maimako bayan sun saki namu."

Kakakin hukumar yan sandan jihar dai, SP Gambo Isah, bai tabbatar da labarin ba tukun.

Source: Legit

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari