Yan bindiga sun afkawa coci ana cikin ibada, sun kashe mutum 1, sun sace 3


Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan fashin daji ne sun kai hari kan wani coci a jihar Kogi, inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da masu ibada guda uku, Punch ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi a Cocin ECWA da ke Okedayo na garin Kabba, hedkwatar karamar Hukumar Kabba Bunu ta Jihar Kogi.

Lamarin ya fau duk da cewa Gwamna Yahaya Bello ya bayyana jihar a matsayin mafi aminci a Najeriya.

Harin ya faru ne kwanaki bakwai kacal bayan da aka kai hari cibiyar kula da gyaran hali ta tarayya da ke Kabba; da kuma sace wasu manoman kaji guda uku a gonarsu.

An ce masu garkuwar sun kai hari cocin ne yayin da ake gudanar da hidimar ranar Lahadi.

Cocin yana kusa da babban titin Kabba-Okene.

Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, DSP William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa jami’an su na bin sawun wadanda ake zargin.

'Yan bindiga sun sace dalilan jami'a kwanaki kadan bayan sace malamansu

Wasu 'yan bindiga sun sace dalibai 10 na Jami'ar Jihar Abia, Uturu (ABSU) a hanyar Ihube zuwa ABSU, Daily Sun ta ruwaito.

Sace daliban na zuwa ne makonni bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da malaman jami’ar uku a kan hanyar Uturu/Isuikwuato.

Lamarin wanda rahotanni suka ce ya faru tsakanin karfe 5 na yamma zuwa 6 na yamma a ranar Asabar, ya jefa al’ummar jami’ar cikin rudani.

An ba da rahoton cewa motar bas ta jihar Abia da ke jigilar fasinjoji zuwa makarantar, SUV da mota kirar Hilux mallakar wani kamfani an same su babu kowa a ciki a wurin da lamarin ya faru, abin da ke nuni da cewa ba daliban kadai aka sace ba.

Wata majiyar tsaro ta ce kawo yanzu ba a san adadin mutanen da aka sace ba.

Legit Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN