Yan APC sun roki Buhari ya mika kujerarsa zuwa kudancin Najeriya a zaben 2023


Wata kungiya a jam'iyyar APC mai suna South East Mandate (SEM), ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saukaka hanyoyin zabar dan takarar shugaban kasa daga amintattun mambobin jam’iyyar na Kudu maso Gabas a zaben 2023
.

Ta ce manufarta ita ce tabbatar da an samu shugaba daga yankin na Kudu maso Gabas a matsayin wanda zai gaji Shugaba Buhari, Daily Sun ta ruwaito.

Kungiyar ta bukaci jam’iyyun siyasa a Najeriya da su mika tikitin takarar shugaban kasar nan zuwa Kudu maso Gabas bisa adalci, gaskiya da lamiri mai kyau.

'Yan APC sun roki Buhari ya mika kujerarsa zuwa kudancin Najeriya a zaben 2023

Shugaban kungiyar, Sanata Julius Ucha ne ya bayyana wa manema labarai batun bayan taron Majalisar Zartaswarsu ta kasa.

Ya gano rashin amana, tsoro na boye, tuhuma da nuna son kai a matsayin wasu abubuwan da ke jefa yankin Kudu maso Gabas cikin koma baya wajen daidaita siyasar Najeriya.

Ya kuma lissafa gazawar yankin wajen gina tsarin da zai bayyana muradunsu a matsayin wani kalubale ga ci gaban siyasa.

Ucha ya ce Kudu maso Gabas yanki ne mai karfi a Najeriya kuma ya kamata a ba yankin damar samar da shugaban kasa saboda daidaito shine mafi cancanta.

Ya kuma bayyana cewa a shirye suke su hada gwiwa da duk wata kungiya da ke aiki don tabbatar da samar da Shugaba daga Kudu maso Gabas a 2023.

Tsohon minista ya fadi abinda zai hana mutanen kudu maso gabas shugabanci a 2023

Wani tsohon Ministan Ayyuka a Najeriya, Adeseye Ogunlewe, ya ce Kudu maso Gabas ba za su iya samar da shugaban kasar Najeriya na gaba ba saboda ba su da hadin kai.

Ya fadi hakan ne yayin wani shirin Arise TV mai suna 'The Morning Show' a ranar Laraba 11 ga watan Agusta, Punch ta ruwaito.

A cewarsa, babu wani dan takarar da ya fi dacewa ya jagoranci kasar nan a 2023 fiye da tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu - wata sanarwa da Bode George, memba na kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, wanda shi ma ya kasance a cikin shirin.

Ya yi ikirarin cewa rashin iya jagoranci da rashin hadin kai zai yi tasiri kan duk wani dan takarar shugaban kasa na Kudu maso Gabas.

Ya ce:

“Wasu rukunin mutane da suka dace, su ne mutanen Kudu maso Gabas amma suna da matsalar shugabanci.

“Suna da baiwar da suka bazu ko'ina a cikin Najeriya kuma suna iya samun kuri’u da yawa, amma sun basu da hadin kai kwata-kwata. Mutumin Imo, dan Enugu, dan Ebonyi ba za su saurari kansu ba.

“Suna da kudi. Idan suka zauna suka tattara abin da za su iya bayarwa, suna da kudi fiye da kusan kowa a Najeriya.

"Amma kun taba ganin mutum daya daga kudu maso gabas ya ce 'Ina sha'awar shugabancin kasa, zan fara kamfen a duk fadin Najeriya nan da nan, ku tara mani kudi?' Kuma ya yi tasiri ga tsarin jam'iyya?"

Bayan Fitowa Daga Taro, Gwamnonin APC Sun Bayyana Matakin da Suka Dauka a Kan Shugaban APC Mai Mala Buni

A wani labarin, Gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki sun kaÉ—a kuri'ar amincewa da kwamitin rikon kwarya wanda takwaransu gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, yake jagoranta, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnonin sun bayyana cewa hukuncin da kotun koli ta yanke a kan zaɓen gwamnan jihar Ondo ya nuna cewa kwamitin na kan doka.

Gwamnonin sun yi wanna jawabin ne a taron da suka gudanar ranar Litinin domin tattauna matsalolin da suka taso a jam'iyyar.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN