Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya yi gargadin a kula game da komawar 'yan bindigan da yunwa ta fatattaka, zuwa garuruwa da yankuna don satar kayayyakin gona kafin lokacin girbi, Daily Nigerian ta ruwaito.
Gwamnan ya yi gargadin ne a ranar Talata 21 ga watan Satumba, a Katsina, a wani taron shawari da ya yi da Ministan Yada Labarai da Al'adu, Lai Mohammed kan yanayin tsaro a jihar.
Taron ya samu halartar Shugabannin hukumomin tsaro na jihar, sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa da na addini, kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.
Source: Legit
Rubuta ra ayin ka