Yadda yan bindiga suka sace sarkin Bungudu a hanyar Abuja


Wasu Æ´an bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace sarkin Fulanin Bungudu, da ke jihar Zamfara a arewacin Najeriya, mai martaba Alhaji Hassan Attahiru.

Ƴan bindigar sun sace sarkin ne kan hanyarsa daga Kaduna zuwa Abuja, kamar yadda ɗaya daga cikin ƴaƴansa da kuma basaraken masarautar Zannan Bungudu Hon Abdulmalik Zubairu ya tabbatarwa BBC.

Bayanai sun ce an kashe É—aya daga cikin jami'in Æ´an sanda a musayar wutar da Æ´an bindigar suka yi jami'an tsaron da ke tare da sarkin cikin mota a hanyar Abuja.

Sarkin yana cikin sarakunan Zamfara masu daraja ta É—aya.

Babu dai wata sanarwa daga rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna, yankin da al'amarin ya faru.

Sace sarkin wani babban ƙalubale ne musamman a daidai lokacin da aka ɗauki mataki na toshe layukan sadarwa da hana cin kasuwannin mako domin maganin ƴan bindiga masu kai hare-hare- da satar mutane.

"Muna tare da shi jiya a Abuja, ya tafi Gusau kuma yana kan hanyar shi ta dawo wa daga Kaduna aka kira mu aka ce an sace shi," in ji daya daga cikin manyan 'ya'yansa.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN