Yadda wani karamin yaro ya mutu cikin rijiya a wata jihar arewa


Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani yaro mai shekara 5 bayan ya fada cikin rijiya a garin Zangon Dinya da ke karamar hukumar Bagwai.

Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito cewa Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Abdullahi ya tabbatar da haka a wata Takarda da ya raba wa manema labarai a Kano.

Ya ce lamarin ya faru ne ranar Alhamis da dare. Ya ce sun sami kiran gaggawa daga wani mai suna Muhammed Usman da karfe 8:30 na dare a ofishinsu da ke Bichi.

Sakamakon haka suka gaggauta zuwa wajen da lamarin ya faru. Sai dai jami'an sun ciro gawar yaron kuma sun mika gawar ga shugaban Mazabar Zangon Dinya Bagwai , Malam Yahaya Sule.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari