Alkalin Kotun shari'a ta 1 da ke Nassarawa a garin Birnin kebbi ta tura Binta Isah da Mahaifinta Aliyu Isah zuwa asibiti domin a duba lafiyarsu kafin Kotu ta yanke masu hukunci bayan mo a zaman Kotu na ranar Alhamis, sun sake nanata ikirarin da suka yi cewa dan da Binta ta haifa Annabi be.
Alƙali Mu'awiyya Umar Birnin kebbi, ya bayar da wannan umarni ne a zaman Kotun na ranar 2 ga
watan Satumba 2021. Alƙali ya tambayesu cewa ana zarginsu da
1. Hada Baki domin aikata laifi.
2. Tayar da hankalin jama'a.
3. Cin zarafin Addinin Musulunci.
Ya
ce " Mako da ya gabata kun gaya wa Kotu cewa dan Binta mai suna
Muhammadu Basiru Annabi ne. Har yanzu kuna kan zancen? Binta da
Mahaifinta Aliyu sun ce eh"
Sakamakon haka
Alƙali ya bayar da umarni cewa a kai su Asibiti a duba lafiyarsu, sai a
dawo da su mako mai zuwa domin yanke hukunci.
Mijin Binta ya ki shiga cikin lamarin
Rahotanni da shafin labarai na isyaku.com
ya tattaro, sun yi nuni da cewa Binta mahaifiyar Basiru tana da aure.
Sai dai mijinta ya nisanta kansa daga wannan lamari. Mun samo cewa
sakamakon haka ya zare hannunsa ya kyaleta da yan uwanta cikin wannan
matsala.
Mahaifin Binta Malam Aliyu Isah yana goyon Bayan diyarshi
Aliyu
Isah, mahaifi ne ga Binta ba mijinta ba kamar yadda muka sami Labarin
farko. Yaro da Binta ta haifa jikanshi ne. Sai dai Aliyu ya dage cewa
jikanshi Annabi ne.
Hankalin Binta da Mahaifinta a kwance Babu alamar damuwa tare da su.
A
zaman Kotu na ranar Alhamis 2 ga watan Satumba, Binta wacce ke sanye da
Hijabi mai klar ja da digo fari gaba daya, tana rike da danta Basiru da
ta kira annabi. Yana sanye da rigar dinki jampa mai kala shudi mai
duhu.
Mahaifinta Aliyu Isah yana sanye da
babbar riga da hulla mai kalar ruwan kasa mai haske. Yanayi da ya
bayyana a fuskarsu bai nuna damuwa tattare da su ba a zahiri.
Mai
gabatar da kara na yansanda Sgt Faruku Muhammad, mai lambar aiki 493010
ya shigar da kara a madadin Kwamishinan yansandan jihar Kebbi kan Binta
da Mahaifinta Aliyu.
Reported by ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari