Yadda samari 5 Yan jihar Sokoto suka kamu da cutar amai da gudawa suka mutu a cikin mota kan hanyar kai gawar abokinsu (Hotuna)


Wasu samari biyar sun mutu yayin da suke kan hanyarsu daga Lagos zuwa jihar Sokoto domin kawo gawar abokinsu da ya mutu sakamakon cutar amai da gudawa.

Shafin isyaku.com ya ruwaito cewa wadanda suka mutu Yan jihar Sokoto ne da suka je Lagos don ci rani.

Samarin suna zaune ne a Ojota, wuri da annobar cutar ta yi karfi a Lagos.

Sun yi shattar wata motar bas domin su kai gawar abokinsu garinsu Sanyinna a karamar hukumar Tambuwal da ke jihar Sokoto. Sai dai suna cikin tafiya ne sai biyar daga cikinsu suka kamu da cutar kuma suka mutu.

Ardon Sanyinna, Alhaji Shehu Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin. An yi jana'izar su bisa tsarin Addinin Musulunci. Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari