Yadda Amarya ta kashe 'yayan kishiyarta 3 da guba a jihar Yobe,


Potiskum - Hukumar yan sanda a jihar Yobe ta damke wata matar aure yar shekaru 22, Khajida Yakubu, kan laifin kashe 'yayan kishiyarta uku da guba.

Wannan abu ya faru ne ranar Juma'a a unguwar Makara-Huta dake karamar hukumar Potiskuma a jihar, rahoton Leadership.

Yaran sun sha guban ne cikin Shayin da kishiyar mahaifiyarsu ta shirya musu.

A jawabin da kakakin yan sandan jihar Yobe,ASP Dungus Abdulkarim, ya saki, ya tabbatar da cewa an damketa.

A cewarsa, Matar da kanta ta garzaya da yaran asibiti bayan da suka sha Shayin misalin karfe 9 na safe amma uku sun rigamu gidan gaskiya, saura 1.

Dungus yace:

"Tuni dai yan sanda sun kaddamar da bincike domin gano abinda ya faru domin hukuntata."

Yaran da aka kashe sune; Zainab Alhaji Haruna (7), Ahmed Alhaji Haruna (9), Umar Alhaji Haruna (12), da Maryam Alhaji Haruna (11).

Legit Hausa

Previous Post Next Post