Yadda Allah ya saka wa budurwa nan take bayan barawo ya kwace mata wayar salula ya gudu a bainar jama'a


Babu abin da ke da dadi kamar sakayyar Allah nan take ga wanda aka zalunta, shafin laabrai na isyaku.com ya leka birnin Accra a kasar Ghana, inda ya samo mana labarin wani Barawo da Allah ya kama shi nan take, domin dai wannan Barawo ya kwace wayar salula ne daga hannun wata budurwa kuma ya sheka da gudu, amma garin ketare titi, sai wata mota da ke tafe ta buge shi nan take har kafarsa ta kare. Budurwa mai waya ta zo ta dauki wayarta, shi kuma Barawo aka bar shi a nan yana ta kuka cikin radadin ciwo yayin da jama'a suka kewaye shi suna kallo.

 Ka ji yadda ta kasance da Barawon wayar salula, saura da me? sai matasa su dangana su zabi sana'ar yi domin kaucewa tozarta irin wannan.


Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari