Yadda aka tube wasu Yan Mata tsirara aka yi rokon neman ruwa (Hotuna)


An yi wa wasu yara mata shida zigidir an jere su a wani kauye a wata al'ada ta addu'ar roƙon ruwa a yankin tsakiyar Indiya.

Lamarin ya faru ne a wani kauye da fari ya yi wa kaka-gida a yankin Bundelkhand na jihar Madhya Pradesh.

Bidiyon da suka yaɗu a shafukan sada zumunta sun nuna yaran na tafiya tsirara da kota a rataye a kafaɗunsu wacce aka ɗaure kwaɗi a jiki.

Mazauna yankin sun yi amannar cewa gudanar da al'adar za ta sa ubangijinsu ya kawo ruwan sama a yankin.

Hukumar kare hakkin yara ta Indiya ta nemi rahoto kan batun daga hukumar gundumar Damoh, inda kauyen yake.

'Yan sandan Madhya Pradesh sun ce ba su samu korafi a hukumance ba kan lamarin, amma sun ce sun kaddamar da bincike.

"Za mu ɗauki mataki idan har muka gano cewa an tilastawa yaran tafiya tsirara," kamar yadda wani jami'in ɗan sanda DR Teniwar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Press Trust India.

Wasu rahotanni sun ce yaran da aka gani a bidiyon ba su wuce shekara biyar ba, suna tafiya tsirara, sai kuma wasu manyan mata da ke bin su a baya suna waƙe-waƙe.

Tawagar mutanen sun dinga tsayawa a kofar kowanne gida a kauyen inda yaran ke karbar tsabar hatsi, wanda a karshe aka kai shi sadaka ga wani wajen dafa abinci na wajen ibada.

"Mun yi amanna yin hakan zai sa mu samu ruwan sama," kamar yadda wata mata da ke cikin tawagar ta bayyana.

Wani babba a yankin Damoh, S Krishna Chaitanya, ya ce da amincewar iyayen yaran aka yi taron kuma har da su aka yi.

Ya kara da cewa: "A irin wannan lamarin, abin da hukuma za ta iya shi ne kokarin nuna wa mazauna kauyen sharrin wannan camfin da nuna musu cewa hakan ba zai sa su samu abin da suke so ba."

Harkar noma a Indiya ta dogara ne kocokan a kan yawan ruwan saman da ake samu a wasu yankunan, sannan akwai al'adu da dama da ake gudanarwa don roƙon ruwa.

Wasu al'ummomin kan yi wata al'ada ne da ake kira yagnas da ta hada da kunna wuta, wasu kan auri kwaɗi ko jakuna ko kuma su fita suna wake-waken rokon ubangijinsu ya ba su ruwa.


Rahotun BBC Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN