Wasiƙa ta maye gurbin waya a jihar Zamfara


A jerin wasikun mu daga ƴan jaridar Afrika, Mannir Ɗan Ali, tsohon babban editan jaridar Daily Trust a Najeriya ya duba tasirin matakin baya-bayan nan da aka ɗauka don daƙile ƴan bindigar da suka addabi Najeriya- wato toshe layukan waya da intanet.

Short presentational grey line

A shekarun baya-bayan nan, rayuwa a yankunan karkara na jihar Zamfara ta yi wahala.

Kungiyoyin 'yan bindiga masu yawo a kan babura sun mayar da jihar mai girman kilomita 39, 761 - ta fi kasashe kamar Burundi da Lesotho da Rwanda girma- wani fage na kashe-kashen kan mai uwa da wabi da fyade da satar mutane don kudin fansa.

'Yan bindigar na da tsari kuma suna da dabara, mafi yawan lokuta suna sanya kayan sojoji don rikita mazauna kauyuka lokacin kai hari.

Matsalar, wadda ta dade tsawon shekaru, ta bazu zuwa wasu jihohi biyar masu makwabtaka da Zamfara.

An gwada amfani da matakai da dama a Zamfara don kawo karshen ayyukan 'yan bindiga, ciki har da:

Sai dai duka wadannan matakan ba su yi tasiri ba, don haka hukumomin Zamfara a yanzu sun haramta sayar da dabbobi, tare da in kasuwannin mako-mako inda manoma da 'yan kasuwa ke zuwa kasuwanci. Satar dabbobi na daya daga cikin hanyoyin da 'yan bindigar ke samun kudi.

Mataki mafi tsauri da aka ɗauka shi ne kashe duka turakun waya 240 da ke Zamfara.

Da fatan hana ƴan bindigar magana da juna da masu ba su bayanai da kuma tattaunawa da ƴan uwan waɗanda suka sace.

Sannan an ci gaba kai masu farmaki ta sama da ta ƙasa.

1px transparent line

Toshe layukan wayar - wanda ya shafi yankunan da ke kan iyakar Zamfara da wasu jihohi - ya yi mummunan tasiri kan iyalai da sana'o'i.

Ƴan ƙananan abubuwa da ake iya yi cikin sauki ta hanyar buga waya yanzu sai an yi tafiyar wuni guda ake iya yin su.

Wasu kuwa sun koma rubuta wasiƙu. Saboda rashin tsarin gidan waya mai inganci, ana aika wasikun ne ta motocin haya da ke tafiya daga wannan gari zuwa wancan a jihar da sauran sassan ƙasar.

Wani haifaffan garin Zamfara mazaunin Abuja ya shaida mani cewa yana cikin ƙuncin rashin sanin halin da iyalinsa ke ciki.

Sai da wani ɗan uwansa ya zo Abuja kwanaki kaɗan da suka wuce ne ya san halin da gida ke ciki.

Wani kuma ya shaida min cewa yana cikin tsananin damuwar da ya yanke shawarar komawa Zamfara don ganin halin da iyalinsa ke ciki.

An kori ƴan bindigar wani wuri

Sai dai duk da mawuyacin halin da toshe layukan wayar ya jefa mutane, gidajen rediyo a Abuja na goyon bayan mataki.

Map of Nigeria

Wani ɗan Zamfara mazaunin Abuja ya ce gara a jure ɗan ƙanƙanin lokaci na wahala maimakon tashin hankali kullum da ya mayar da Zamfara wani jeji da ƴan bindiga ke mulki.

A halin yanzu kusan babu wanda ya san abin da ke wanzuwa a Zamfara kan yadda jami'an tsaro ke far wa maharan.

Ko ƴan jarida ma ba su da hanyar sanin halin da ake ciki.

Wani ƴar jarida ta shaida min cewa tana ta ƙoƙarin shawo kan hukumomi su ba ta damar aiki tare da dakarun soji.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar da gaskiyarsu ba na nuna cewa an fara samun nasara wajen fatattakar ƴan bindigar daga inda su ke ɓoye a daji.

Sai dai, mafi ɗaga hankali, shi ne ana tunanin ayyukan sojojin sun kora su zuwa jihohi maƙwabta kamar Katsina, mahaifata.

An samu ƙaruwar satar mutane a makon da ya gabata, ciki har da na ƴaƴan wani sananne da kuma wani tsohon ma'aikacin gwamnati tare da yarsa mai shekara 15.

Ni da kaina kwanan nan na ɗauke mahaifiyata daga gidanta- kuma ƴan kwanakin baya da suka wuce aka yi garkuwa da ɗaliban jami'a uku daf da gidan nata.

Masana harkokin tsaro da dama na ganin cewa matakin na yanzu, duk da wahalarsa, kamata ya yi a haɗa da sauran jihohi shidda da ke fama da matsalar tsaro, yadda ƴan bindigar ba za su samu wurin fakewa ba.

Da yawa sun amince sai jihohin sun haɗa kai wurin yaƙarsu sannan za a ga ƙarshen wannan tashin hankalin.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN