Wani matashi ɗan shekara 21 da ake zargin 'ɗan ƙwaya' ne ya kashe mahaifinsa da duka a Kogi


Ana zargin wani saurayi mai shekaru 21 mai suna Muhammad Yusuf da yi wa mahaifin sa, Alhaji Ibrahim Yusuf, dukan tsiya wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa ransa, The Guardian ta ruwaito.

Dama su biyu ne kadai a gidan lokacin da lamarin ya faru a wuraren makarantar firamaren St. Mary da ke Lokoja a daren Laraba.

Makwabciyar Alhaji Ibrahim Yusuf ta magantu kan yadda lamarin ya faru

Kamar yadda makwabciyar su, Miss Bello Nana, ta shaida, tun safiyar Laraba yaron yake iya-shegen sa sannan ta shawarci mahaifin da ya yi gaggawar kai karar sa ofishin ‘yan sanda don ayi saurin kawo karshen lamarin.

A cewar ta, wanda ake zargin wanda ya kammala makarantar sakandare ya murje idon sa ya ki ci gaba da karatu duk da kokarin da mahaifin sa yake yi akan sa, sai shaye-shaye kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

A cewar Nana, a ranar da lamarin zai faru ta tafi aiki karfe 4pm zata taso karfe 12 na tsakar dare sai ta yanke shawarar dawowa karfe 10 na dare. Tayi ta kwankwasa kofa amma babu wanda ya bude.

Sai ita dakanta ta bude kofar kasancewar tana da makullin gidan. Ta tambayi inda Baba yake amma wanda ake zargin ya yi kisan ya ce ba ya nan.

Ta san cewa tsohon ba ya fita in dai karfe 6 na yamma ya yi kuma shi yake rufe kofa amma saurayin ya ce ya fita.

Ya amsa ne a dakin Baban duk da Baban ba ya barin shi shiga dakinsa, daga nan sai zargi ya shiga zuciya ta, take anan na kira saurayi na.

“Mun kira lambar Baba amma a kashe,” a cewar ta, hakan ya sa suka je ofishin ‘yan sanda suka taho da jami’an.

“Bayan mun shiga dakin ne muka gan shi kwance cikin jini amma yana motsi sai muka yi gaggawar wucewa da shi asibiti. Da safen nan muka samu labarin Baba ya rasu,” kamar yadda Nana ta shaida.

'Yan sanda sun tabbatar da kama wanda ake zargin

An bukaci jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, DSP Williams Aya, ya ce an kama wanda ake zargi.

A cewarsa:

“Mun samu labari da misalin 9pm na jiya cewa DPO da Division A na ofishin ‘yan sanda da ke Lokoja cewa wani Muhammad Yusuf mai shekaru 21 da ke kusa da makarantar firamaren St. Mary a Lokoja ya kai wa mahaifin sa farmaki

“Take anan ‘yan sanda suka nufi inda lamarin ya faru suka sami Yusuf Ibrahim cikin jini da raunuka a kan sa."

Wani mutum ya gamu da ajalinsa yayin da ya shiga maƙabartar musulmi cikin dare don haƙo gawa

A wani labarin daban, wani mutum da ba a gano ko wanene ba ya mutu yayin da ya ke yunkurin hako gawa a makabarta da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Premium Times ta ruwaito.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a makabartar musulmi da ke Iberekodo, karamar hukumar Abeokuta ta Arewa na jihar Ogun.

Abimbola Oyeyemi, mai magana da yawun yan sandan jihar Ogun, ya tabbatarwa Premium Times afkuwar lamarin a ranar Laraba.

Source: Legit

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE