Wadanda ake zargi sun sanar da dalilinsu na sacewa da sheke mahaifin tsohon gwamna



Makasan Pa Defwan Dariye, mahaifin tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye sun bayyana cewa sun yi garkuwa da shi ne don su samu kudade daga hannun dan sa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin ya ce Jethro Nguyen mai shekaru 53 dan asalin Bakos da ke jihar Filato ne ya hallaka Dariye.

Daya daga cikin su mai suna Sunday Ibrahim, ya kara tabbatar da cewa Nguyen ne wanda ya shirya komai don shi yayi hayar mutane 10 don su yi garkuwa da tsohon har fadar sa.

Bayan an kwashe su zuwa hedkwatar tsaro da ke Abuja, kakakin rundunar ‘yan sandan, Frank Mba ya bayyana cewa, Pa Dariye mai shekaru 93 ya shiga cikin mawuyacin yanayi a hannun masu garkuwa da mutane na tsawon kwana 8.

A cewar sa, sun cigaba da ciniki bayan biyan masu garkuwar naira miliyan 10 don su sake shi, amma sai da suka hallaka shi, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar Mba, lamarin ya faru ne a watan Yunin 2020 inda ya kara da cewa an tsinci gawar ne sai aka umarci jami’an bincike na sirri su fara aikin su.

“Laifin na rashin imani ne. Sun azabtar da shi sakamakon matsayin sa da shekarun sa, horon ya yi masa yawa.”

“Sun ki barin tsohon ya tafi gida suka cigaba da cutar da shi duk da sun amshi naira miliyan 10 amma sai da suka hallaka Pa Dariye.

“Cikin kwana 30 ‘yan sanda sun samu nasara mai tarin yawa har sun kama mutane 8 wadanda suke da hannu dumu-dumu a hallaka mahaifin tsohon gwamnan.

“Duk wadanda ake zargin, in ban da kadan cikin su duk ‘yan kauye guda ne a karamar hukumar Bukkos har da shi mamacin. Kilan hakan ne dalilin da yasa suka hallaka tsohon saboda bakar hassada.”

Kakakin hukumar ‘yan sandan ya ce, cikin wadanda ake zargin an kama 3 a ranar 28 ga watan Augusta a wani gari wanda iyaka ne tsakanin Jihar Nasarawa da Taraba.

An kwashe watanni ana bincikarsu ana yi musu bin diddiki sakamakon bin masu sayen makamai, ta’addanci, fashi da makamai da sauran su.

A cewarsa, za a tura wadanda ake zargin zuwa kotu don ta yanke musu hukunci.

Yajin aiki: FG ta ce babu likitan da ke bin ta ko naira daya

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya a ranar Talata ta musanta batun da ke cewa ta na rike da albashin likitoci da sauran ma’aikatan lafiya inda ministan kwadago ya ce zancen kanzon kurege ne.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige ya bayyana hakan a wani taro na kwamitin gwamnatin tarayya a kan albashi tare da shugabannin kungiyoyin ma’aikatan lafiya.

Ngige ya ce, wadannan karairayin daga kungiyar likitoci masu neman kwarewa ne ta NARD, wadanda suke hana kowa ganin kokarin gwamnatin tarayya a kan harkar lafiya.

Source: Legit.ng

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN