Tashin hankali: An tsinci gawar budurwa cikin motar basarake, ya cika wadonsa da iska


Hankulan mutane ya tashi a jiya a harabar asibiti kwararru na jihar Edo da ke Sapele Road a Benin yayin da aka gano gawar wata budurwa rufe cikin wani basarake da aka sakayya sunansa kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

Faruwar lamarin ya jefa iyalan budurwar mai shekaru 27, mai suna Faith Aigbe cikin alhini.

Yan uwa da iyalan matar da ta riga mu gidan gaskiya sun taru suna cike da bakin ciki a yayin da gawar ta ke rufe cikin motar kamar yadda rahoton na The Guardian ya bayyana.

A cewar wasu daga cikin 'yan uwan marigayiyar masu suna Mrs Janet Asemota da Mercy Eddy, sun yi ikirarin cewa basaraken ne ya kawo Faith asibitin.

Sun ce bayan ya gano ta mutu, basaraken sai ya rufe motar mai bakin gilashi kirar Lexus SUV ya kuma tsere.

Wata kawar marigayiyar da sauran 'yan uwanta sun rika sharbar kuka suna neman a bi musu hakkin su.

Yan sanda daga Aideyan sun iso wurin da abin ya faru sannan suka dauki motar tare da gawar.

Har cikin silin na ke ɓoye kuɗi amma tana shiga ta sace: Miji ya nemi a raba aure don satar da matarsa ke masa

Rahotun Jaridar Like

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari