Rikici ya barke a yankin Sapele, Karamar Hukumar Sapele ta jihar Delta yayin da ‘yan kasuwa Hausawa da Fulani makiyaya a yankin a ranar Litinin suka yi artabu da kare-jini-biri-jini a Kasuwar Hausa da ke kan hanyar Benin zuwa Warri, Amukpe, a cikin birni.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce akalla mutane goma ne suka samu munanan raunuka a cikin farmakin da ya biyo baya sannan aka garzaya da su asibitoci daban-daban a yankin, in ji rahoton Daily Report Nigeria.
Punch ta ruwaito cewa, an lalata shagunan katako, lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa yayin da wasu masu ababen hawa suke tsere suka bar ababen hawansu domin tsira.
Source: Legit