Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid


Babban limamin masallacin Juma’a na Apo Legislative Quarters dake Abuja, Sheikh Muhammad Khalid, kwanan nan ya yi fice a kafafen sada zumunta bayan faifan bidiyon wa’azin sa da ya soki shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya bazu.

A cikin wata hirar da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar Punch, malamin addinin Islaman ya ce yana tsaye kan kalamansa cewa shugaban bai tsinana komai ba.

A tattaunawar, malamin ya bayyana abubuwan da suke damunsa game da gwamnatin shugaba Buhari, wadanda a cewarsa gwamnatin ta cika yiwa 'yan Najeriya karerayi.

A bangare guda, ya kuma bayyana cewa, addininsa ya horar da shi da fadin gaskiya da adalci, don haka dole ne ya fadi gaskiya game yadda mulkin Buhari yake kamar yadda ya yi a lokacin Jonathan.

Abubuwa a fili sun nuna Buhari ya gaza

Da wakilin jaridar Punch ya tambaye shi shin yana da wata matsala da gwamnatin Buhari ganin yadda ya caccaki shugaban a wani bidiyo? malamin ya amsa da cewa:

"Halin kasar ya sanar da haka, kuma ina kan hanya madaidaiciya domin addinina ya horar da ni da yin adalci kuma dole na yi.

"Idan na fadi irin wadannan abubuwa a lokacin (Goodluck) Jonathan amma ba na son in fade su yanzu saboda ina addini na daya da Shugaban kasa, to ni munafuki ne.

Kisan kare dangi ake a Najeriya

Da yake kokawa kan yadda kashe-kashe ke kara yawa a kasar, malamin ya bayyana cewa, halin da ake ciki ya yi kama da shirin kisan kare dangi irin wanda ya faru a kasar Rwanda.

Hakazalika, malamin ya ce an fi kashe mutane da yawa a wannan mulkin na Buhari fiye da mulkin Jonathan, lokacin da shugaba Buhari ya yi alkawarin dawo da zaman lafiya a kasar.

A cewarsa:

"Na je Rwanda na ga abin da ya faru a can. A Najeriya, hakika muna wasa da wuta.

"Kashe-kashen da ake yi a kasar na daukar salon kisan kare dangi kuma shi ya sa mutane ke mutuwa a kullum.

"Ana kashe mutane da yawa a wannan mulkin fiye da na gwamnatin da ta gabata.

"Ku yi binciken ku kuma kwatanta shi tare da adadin mutanen da aka kashe a cikin gwamnatin da ta gabata."

Mun yi ta addu'a ba mu ga sakamako ba

Da aka tambaye shi shin a matsayinsa na malami ba addu'a ya kamata ya yi ba malamin ya amsa da cewa:

"Gaskiyar ita ce ba za mu iya musanya ayyuka da addu'o'i ba. Amma yi masa addu’a ya yi me? Zan yi masa addu’a ne don ya dauki mataki, ba wai ya yi watsi da nauyin da ke kansa ba.

"Addu'a ba ta aiki a haka kuma shi ya sa na ce idan yana da burin cika alkawuransa, Allah ya taimake shi. Baya ga haka, mun jima muna yi masa addu’a, menene sakamakon?

Legit Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN