Matsalar tsaro: Jihohin Arewa 7 sun hada kai zasu ɗauki jami'an tsaro 3,000, Masari


Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, yace jihohi 7 a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya sun amince su ɗauki yan bijilanti 3,000 domin taimakawa wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Masari ya faɗi haka ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wurin taronsa da ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, da sarakunan gargajiya.

Tribune Online ta ruwaito Gwamnan na cewa rundunar yan sandan ƙasar nan ce zata horad da yan bijilantin da za'a ɗauka aiki.

Wane jihohi ne suka amince da haka?

A cewar Masari, Gwamnonin jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi Kaduna, Neja, Katsina da kuma Nasarawa sun gana kuma sun amince su ɗauki jami'an domin taimakawa hukumomin tsaro magance matsalar tsaro a jihohin.

Masari yace:

"A maadadin gwamnonin waɗannan jihohin da na ambata, ya kamata ace sun halarci wannan taron amma ni zan wakilce su baki ɗaya."

"Ayyukan yan bindiga a arewa maso yamma da arewa ta tsakiya ya zama babbar matsala, saboda haka mun ɗauki wasu matakai don kawo ƙarshen lamarin. Akwai ƙungiyoyin yan bindiga sama da 150 a dazuka.

"Waɗannan mutanen ba su da aƙida mai kyau, addini ko wata manufa, kawai duna rayuwa ne kamar dabbobi."

Yan bindiga sun shiga halin tasku

Gwamna Masari ya ankarar cewa wasu miyagun yan bindiga sun fara yawo ƙauyuka domin satar amfanin gona yayin da ake gab da girban kayan gona.

Saboda yunwa yan bindiga sun fara zuwa ƙauyukan dake kusa dazuzzuka. Dun san lokacin girban amfanin gona ya zo, saboda haka manufar su ita ce su saci kayan abincin da manoma suka noma."

A wani labarin na daban kuma

Source: Legit.ng

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN