Duba matakan da za ku bi don zama da kawaye lafiya


Kowa a duniya na bukatar ƙawa, domin abokai nagari tamkar duwatsun alfarma suke, don suna taimaka mana a rayuwarmu.

Sai dai fa ki sani, yadda kike bukatar kyautata zamantakewarki da miji da iyaye da dangi, haka ma kike bukatar sanin matakan kyautata zamantakewarki da kawaye.

Kamar yadda muka sani, zamani ya zo mana da ci gaba fasaha da ya samar da shafukan sada zumunta, wadanda ke taimakawa wajen gyara zamn tare na kawaye.

Saboda a yau an zo gabar da kujuba-kujubar yau da kullm kan sa mu dade ba mu gamu da juna ba, don haka saboda gudun zargin girman kai daga kawayen da kuka taso tare, ya kamata a dinga tuntubar juna a kalla ta irin wadannan hanyoyin.

Idan kina dakawayen da ke taimakon rayuwarki ta hanyar sa ki farin ciki da taimaka wa lafiyar kwakwalwarki, to akwai wasu matakai da ya kamata ki bi don inganta zamantakewarku.

Amma kafin nan, bari mu duba mu ga wace ce ma kawa, kuma da wa ya kamata a yi kawance?

A lokuta da dama idan ba ki yi taka tsantsan wajen tara kawaye barkatai da kuma iya zama da su ba, kina zaune wata rana za ki ji wata kawarza ta ha'ince ki ko ta ci amanarki ta hanyoyi da dama.

Kuma ba yadda za ki yi sai dai ki dau hakuri, wanda ka iya haddasa maki tsananin damuwa.

Wace ce kawa?

Kawa ita ce mai son ki tsakani da Allah ba don wani abu da kika mallaka ba, wacce za ta tsaya miki a al'amuranki duk runtsi.

Kawa ta gari ita ce wacce ba za ta juya miki baya ba ko da kin samu kanki a wani sammatsi. Mai tsayawa ta taya ki kuka lokacin bakin ciki, ta kuma taya ki dariya lokacin farin ciki.

To wane irin zama ya kamata ki yi da kawayenki?

Kawa ta gari ita ce mai rike amana, mai gaya miki gaskiya ko da tana da daci, sannan ko kin yi fushi da ita kan hakan ita ba za ta yada ke ba.

Matakan gyara zamantakewa da kawaye

1. Ki tabbatar kuna tunyubar juna akai-akai, dadewa ba a hadu ba ko dadewa ba a yi magana ba kan sa zuciyoyi su yi nauyi su ji kamar kun yada juna ne.

Kowacce za ta dinga zargin dayar ta yada ita ko sauyi rayuwa ya sa ta manta.

2. Yin taka tsantsan da gudun wuce gona da iri

Ku dinga taka tsantsan da gudun tunzura juna, bai kamata ku dinga saurin hasala ba nan da nan. Idan kuka yi wa juna laifi, to ku warware ku sasanta ba tare da wani ya ji ba.

Sannan ku sani a kowane lamari da kowace mu'amala akwai iyakoki, kuma ya kamata a kula da su kar a ketare su kar a take su.

Kar ki zakalkale da shiga wasu lamuranta musamman wadanda ba ta saki a ciki ba, sannan kar ki dinga zuga ta a kan abubuwan da kika san ba daidai ba ne, kamar hidimarta ita da mijinta.

3. Ki guji bude cikinka ga sabuwar kawa

Musamman ma dai kawar da aka hadu a shafukan sada zumunta. Irin wannan akwance yawanci na je-ka na yi ka ne. Don haka wauta ce babba ki saki jiki da baki da sabuwar kawar da ba ki gama karantar ta ba, amma hakan ba ya nufin ki ki karbar kawancenta.

4. Ku zama masu kyautata wa juna ta kowane bangare. Yi wa juna abin alheri da tsaya musu a kan lamurransu.

Kar ku sanya gasa tsakaninku, hakan na jawo kyashi da hassada da bakin ciki, lamarin da ka iya kai wa ga cin amana.

5. Kar ki yarda rudin kawance ya jawo ki dinga kin mayar da hankali wajen bai wa mijinki hakkokinsa. Don sau da yawa wasu kan fifita kawaye fiye da yadda suke fifita mazajensu.

Hakan na iya sa wa idan kawar mara tsoron Allah ce ta raina ki ta kuma samu damar cin amanarki ta haka, ta hanyar hada shi da kanta ko wata ta jikinta da za su iya aure shi, saboda ai ta fahimci cewa yana rasa wasu abubuwan a tare da ke.

Rahotun BBC Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN