Makaman yaƙin Amurka da Taliban ta samu ganima


Wasu hotuna sun bayyana da ke nuna mayaƙan Taliban a wajen kayan yaƙin da dakarun Amurka suka bari a babban filin jirgin sama na Hamid Karzai da ke Kabul.

Dakarun Amurka sun bar jumullar kayayyaki da suka haɗa da jiragen yaƙi 73 da motoci kusan 100 da sauran kayyayaki, a yayin da suka gama janyewa daga ƙasar ranar 31 ga watan Agusta.

Amma Shugaban Cibiyar Sojin Amurka Janar Kenneth McKenzie ya ce duk an lalata kayayyakin ta yadda ba za a iya amfani da su ba.

Ya ce, "waɗannan jirgin ba za su iya tashi sama ba."

Jiragen yakin da aka bari a Kabul sun haɗa da:

A watan Yuni, dakarun Afghanistan na amfani da: a

Zai yi wahala a faɗi kuɗaɗen kayayyakin kai tsaye - amma kuɗin jirgi samfurin A-29 kawai ana cewa ya kai dala miliyan 10.

Wani bidiyo da wakilin jaridar LA Times Nabih Bulos ya ɗauka ya nuna mayaƙan Taliban a cikin wani helikwafta samfurin CH-46 Sea Knights .

Ma'aikatar Tsaro ta Amurka ta bar helikwafta samfurin Sea Knights bakwai a Afghanistan bayan da ta yi amfani da su bayan kammala kwashe ma'aikatan ofishin jakadancinta a Kabul.

Sannan an ga hoton wani jirgin yaƙi samfurin C-130 a yashe a filin jirgin Hamid Karzai.

A cewar Janar McKenzie, an kuma bar motocin yaƙi da nakiyoyi ba sa yi mata komai (MRAP) guda 70, bayan lalata ta.

An ambato cewa kuɗin kowace motar MRAP daya za ta kai daga tsakanin dala 500,000 zuwa dala miliyan.

Sannan a Kabul an bar:

A wasu lamurran an yi amfani da bama-bamai don lalata kayayyakin ta yadda ba za su moru ba.

A wani wajen daban a ƙasar, dakarun Afghanistan sun tsere ba tare da yin ƙoƙarin lalata makaman ba.

Hotunan da tauraron ɗan adam ya ɗauka sun nuna cewa an fice da wasu jiragen yaƙin zuwa ƙasar Uzbekistan, kwanaki kaɗan kafin rushewar gwamnatin Afghanistan.

Ƙwararru sun ce Taliban ba za su mori mafi yawan jiragen yaƙin ba ba tare da suna da ƙwararrun matuƙa ba, da kuma gyaran su da samun wasu ɓangarori idan sun lalace.

Amma, duk da cewa zai yi wahala a gano adadin, yawanci cikin jirage 167 ɗin, da suka haɗa da helikwafta samfurin UH-60 guda 33, da ke ƙarƙashin ikon dakarun Afghanistan a ƙarshen watan Yuni, a yanzu ana tsammanin suna hannun Taliban.

Kuma tuni ƴan Taliban suka fara amfani da wasu makaman na Amurka.

An ɗauki hoton dakarun Taliban na musamman a Kabul suna ɗauke da manyan bindigogi samfurin M4.

Sannan Amurka ta samar da fiye da manyan motocin yaƙi 2,500 daga watan Disamban 2017 zuwa Afrilun 2020, a cewar Babban Mai Kula da sake gina Afghanistan na musamman na Amurka.

Ainihin kudin ya bambanta - amma an ambato cewa kuɗin duk guda daya ya zarta dala 250,000.

Ƙwararru sun ce sauran kayayyakin za su iya yi wa Taliban matuƙar amfani ciki har da tabaron da ake amfani da shi da daddare don hango nesa, wadanda aka bai wa dakarun Afghanistan irin su 16,000 daga tsakanin shekarar 2003 da 2021.

BBC Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN