Ku kashe yan bindiga ko da sun shiga cikin jama'a - Gwamna ya gaya wa soji


Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya roki sojoji kada su tausaya wa yan bindiga ko ina suka gansu, su buɗe musu wuta, kamar yadda Amniya Hausa ta ruwaito.

Gwamnan yace matakan da aka ɗauka sun jefa rayuwar yan bindigan cikin mawuyacin hali, inda a yanzun suke ƙoƙarin shigowa cikin mutane

Amma Masari ya bukaci dakarun sojojin kada su tausaya musu koda sun shiga cikin mutane a bude musu wuta, ko da hakan zai ritsa da mutanen da ba ruwansu.

Sai dai Masari ya roki jami'an sojin su ɗauki wasu matakan kariya ga mutanen idan irin haka ta faru, gudun kashe waɗanda ba ruwansu da yawa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Gwamna Masari ya yi wannan furucin ne yayin da ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya ziyarce shi, domin samun bayanai kan irin nasarorin da ake samu a yaƙi da yan bindiga.

Ba maganar sulhu da yan ta'adda

A nasa ɓangaren, Ministan yace:

"Daga yanzun gwamnatin tarayya ba zata amince da yin sulhu da yan bindiga da yan ta'adda ba."

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumuni Kabir Usman, yace ba dai-dai bane tattaunawar sulhu da irin waɗannan mutanen.

Waɗannan mutanen ba su da addini, ya kamata a haɗa karfi da karfe kuma a ɗauki duk matakan da ya dace domin kawar da su baki ɗaya."

Legit Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN