Kamfanin iPhone ya kera iPhone 13 Pro Max, wayar da ba a taba irinta ba a fasaha


Babban kamfanin fasaha na Apple ya sanar da kirkirar sabuwar waya mai suna iPhone 13 Pro, irinta na farko wanda ke ba da ma'ajiyar bayanai Terabyte daya (1TB), yana bawa masu amfani da iPhone damar adana bayanai kwatankwacin na iPhone 13 sau biyu.

An sanar da sabon samfurin yayin taron yanar gizo da kamfanin a ranar Talata 14 ga watan Satumba, in ji rahotom Peoples Gazette.

Kodayake kamfanin fasahar a baya ya daura ma'ajiyar bayanai 1TB a kan iPad, samfuran iPhone suna da adadin ajiyar da a kai 512GB.

Greg Joswiak, Babban Mataimakin Shugaban kamfanin Apple shashen tallace-tallace na duniya, a wurin taron ya bayyana cewa:

"IPhone 13 Pro da iPhone 13 Pro Max sune mafi kyawun samfuran iPhone na yau da kullum tare da mafi girman ci gaba a tsarin kyamarar mu, mafi kyawun kargin batir a cikin iPhone, da mafi kyawun wajen saurin aiki, saita sabon ma'auni na iPhone da ba da damar abubuwan ban mamaki da ba a taba yi ba."

Apple kuma ya ba da sanarwar yana habaka ma'ajiyar iPhone akan daidaitattun samfuran sa.

Ya batun farashi?

Farashin farko na iPhone a ranar fitar da ita zai fara a $999 kuma za a fara jigilar ta a ranar 24 ga Satumba. Zabin 1TB akan iPhone 13 Pro zai sauki farashin $1,499 da $ 1,599 akan babban iPhone 13 Pro Max.

Sabuwar iPhone din na da jerin sabbin abubuwan ingantayya da sabuntawa wadanda suka hada da karamin kira, sabbin fasalolin kyamara wadanda ke ba masu amfani sigar bidiyo na yanayin hoto da zabin daukar bidiyo mai inganci da ake kira ProRes.

Za a iya samun iPhone 13 Pro da iPhone 13 Pro Max a cikin launuka hudu; ruwan toka, ruwan zinariya, ruwan azurfa, da shudi, kamar yadda CNET Tech ta ruwaito.

Legit Hausa

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN