Jiragen yakin Najeriya sun yi wa yan bindiga luguden wuta mai muni a dajin Zamfara


Gwamnatin Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta yi ikirarin cewa jiragen yaƙin rundunar sojin saman kasar sun yi luguden wuta kan fitattun sansanonin 'yan fashin daji a jihar da ma kewaye. Shafin BBC Hausa ya ruwaito.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ta ba da sanarwar rufe abin da ta kira haramtattun tasoshin mota da wasu kasuwanni nan take a faɗin jihar.

Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara Ibrahim Dosara ya fitar ta ce sansanonin da aka tarwatsa a hare-haren sojin saman Najeriya sun haɗa da wani ƙasurgumin ɗan fashin daji da ake kira Dan ƙarami a ƙaramar hukumar shinkafi

A cewar sanarwar a baya ɗan fashin dajin ya fitar da wani bidiyo yana murna bayan artabun da suka yi da sojoji.

Mahukuntan jihar Zamfara sun kuma ce sojojin ƙasa sun yi wa wasu 'yan fashin daji da suka yi kokarin tserewa bayan luguden wutar kwanton-ɓauna.

A baya bayan nan ne gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da umarnin toshe hanyoyin sadarwa a jihar, wanda yana cikin matakan da hukumomin suka ɗauka domin magance matsalar tsaro a jihar.

Haka kuma gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da umarnin rufe dukkanin abin da ta kira haramtattun tashoshin mota da kasuwanin gefen titi a faɗin jihar, musamman waɗanda ke kan titin Ƙaura-Namoda da mahaɗar lambar Bakura da mahaɗar kwanar Manyanci da kuma Anka.

Sauran sun hada da garejin Mai-lena da kasuwar shinkafa da kayan gwari ta filin jirgi a birnin Gusau.

Sai dai wasu masana sun nanata bukatar ganin cewa hukumomin Najeriya sun haɗa ƙarfi da ƙarfe da ƙasashe maƙwabta domin matakan su yi tasiri.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE