Jerin jihohi 21 da Buhari ya kai ziyarar aiki tun bayan hawansa mulki a 2015


Tun bayan nasarar lashe zaben shugabancin kasa da Muhammadu Buhari ya yi a 2015, ya ziyarci jihohi 21 daga cikin 36 na kasar nan domin aiki, The Nation ta tabbatar da hakan.

Borno ce jihar da ta'addanci ya fi katutu kuma ita ce jihar da ya fi kai ziyara tun bayan hawan shi mulki.

Shugaban kasa muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Borno a 2017, 2018, 2019, 2020 da 2021

Ga jerin jihohin da shugaban kasan ya ziyarta tun bayan hawansa mulki domin aiwatar da ayyuka:

Adamawa - A ranar 20 ga watan Fabrairun 2018, Buhari ya halarci gagagrumin taron yaki da rashawa na jihar Adamawa.

Bauchi – A ranar 26 ga watan Afirilun 2018, Buhari ya ziyarci jihar Bauchi inda ya kwashe kwanaki biyu na aiki.

Benue – A ranar 12 ga watan Maris na 2018, Buhari ya ziyarci jihar Benue.

Borno – Duba da halin rashin tsaron da jihar ke ciki, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar sosai.

Bauchi — Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Bauchi kuma ya samu tarba ta musamman daga tsohon Gwamna Muhammad Abubakar inda aka kaddamar da asibitin sojin sama kuma an kaddamar da raba wa manoma kayan tallafi.

Cross River — A ranar 26 ga watan Yunin 2018, shugaban kasa ya ziyarci Calabar.

Ebonyi — A ranar 14 ga watan Nuwamban 2017, Buhari ya isa jihar Ebonyi domin aiki, ziyara ta farko irin ta tun bayan da hau shugabancin kasa.

Edo — Jihar Edo ce jihar farko ta kudu kudu wacce shugaban kasan ya kai ziyara ranar 8 ga watan Nuwamban 2016 bayan gayyatarsa da Gwamna Adams Oshiomhole ya yi domin kaddamar da wasu ayyuka.

Jigawa — A ranar 14 ga watan Mayun 2018, Buhari ya ziyarci jihar Jigawa inda ya sauka a babban birnin Dutse na kwanaki biyu. Ya samu tarba ta musamman daga Abubakar Badaru na jihar Jigawa da Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano inda ya kaddamar da wasu ayyuka.

Kaduna — Buhari ya ziyarci jihar Kaduna a ranar 5 ga watan Janairun 14, 2018 inda ya kaddamar da sabbin jiragen kasa.

Kano – A ranar 5 ga watan Yulin 2021, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci Kano inda ya kaddamar da aikin dogo na Kano zuwa Kaduna, wani sashi na dogon Kano zuwa Legas. Ya kuma kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar Kano ta aiwatar.

Katsina — Bayan kwashe kwanaki a Kano, Buhari ya karasa Katsina, jiharsa. Ya kaddamar da aikin samar da ruwa na yankin Zobe da titin Tsaskiya a Safana.

Lagos - Bayan gayyatar da tsohon Gwamna Akinwumi Ambode ya yi wa Buhari zuwa Legas, ya ziyarci jihar a ranar 24 ga watan Afirilun 2019. Ya kaddamar da wasu jerin ayyuka.

Nasarawa — Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Nasarawa a ranar 8 ga watan Fabrairun 2019. Ya kaddamar da aikin wata makaranta a Lafia, cibiyar lafiya ta Kwandere da kuma babbar kasuwar Muhammadu Buhari a Karu da sauransu.

Ondo — A ranar 5 ga watan Fabrairun 2020, Buhari ya ziyarci jihar Ondo inda ya kaddamar da gagarumar cibiyar kasuwanci ta Ondo da gadar sama.

Osun — Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar a ranar 1 ga watan Satumban 2016 domin kaddamar da wasu ayyuka daga cikin shagalin cikar jihar shekaru 25 da kafuwa.

Plateau — A ranar 8 ga watan Maris na 2018, shugaban kasa ya ziyarci Jos inda ya kaddamar da wasu tituna da suka hada da babbar hanyar Mararaba da sauransu.

Rivers — A ranar 25 ga watan Oktoban 2018, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani bangare na filin auka da tashin jiragen sama na Omagwa da ke Ribas.

Taraba — Buhari ya ziyarci Taraba a ranar 5 ga watan Maris din 2018 domin duba rikicin makiyaya da manoma wanda ya janyo jama'a da dama suka rasa gidajensu.

Yobe — A ranar 14 ga watan Mayun 2018, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyaci Damaturu, jihar Yobe.

Zamfara — Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Zamfara a ranar 22 ga watan Maris din 2018 domin duba wasu lamurran tsaro da suka hada da 'yan bindiga.

Imo – A ranar Alhamis, 9 ga watan Satumban 2021, shugaban kasa Buhari ya ziyarci jihar Imo domin aiwatar da wasu ayyuka, karon farko tun bayan hawansa shugabanci kasa a 2015. Ya kaddamar da wasu ayyuka a jihar.

Source: Legit Newspaper

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE