Jama’ar gari sun kashe wani da ake zargin dan fashi ne a Katsina

Rahotanni sun bayyana cewa mazauna garin Magama a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina sun yi nasarar kama wani mutum da ake zargi dan fashi ne.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa dan fashin, wanda aka bayyana sunansa a matsayin Baleri, ya badda kamanni don siyan wasu magunguna a cikin garin.

Sai dai kuma, wasu mazauna garin sun gane shi sannan kuma suka far masa, amma a karshe kungiyar 'yan banga ta cece shi inda aka ce sun mika shi ga sojojin da ke sintiri a yankin.

Daga baya an ce an ga gawarsa a kusa da kauyen Kukar Babangida na karamar hukumar guda, amma babu cikakkun bayanai kan yadda a karshe ya mutu.

Jaridar Aminiya ta kuma ruwaito cewa jami'an 'yan sanda sun cafke 'yan uwansa guda uku da suka zo daukar gawarsa don yi masa jana'iza.

Wannan na zuwa ne yayin da aka dakatar da sabis na wayar sadarwa a wasu kananan hukumomin jihar, ciki har da Jibia.

Sauran kananan hukumomin da ke fama da matsalar rashin sabis sun hada da Faskari, Dandume, Funtua, Malumfashi, Bakori, Dutsin-Ma da Barsari da sauransu.

Legit Nigerian

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN